An Yi Wa Wata Yarinya Bulala 80 Bisa Laifin Shan Tabar Wiwi

0
629

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WATA kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Magajin Gari ta jihar Kaduna, ta yanke wa wata budurwa mai shekaru 19 a duniya, Zainab Abdullahi, hukuncin bulala 80 biyo bayan kama ta da laifin shan tabar wiwi a bainar al’umma.

Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Alhamis, Alkalin kotun Malam Muhammad Shehu Adamu, ya zartar da wannan hukunci a kan Zainab bayan ta amsa laifin da ake zarginta da aikata wa na shan tabar wiwi a filin Allah.

Alkali Shehu ya ce bulala 80 shi ne hukuncin da shari’a ta yi tanadi ga duk wanda aka kama da laifi makamancin wanda Zainab ta aikata na shaye-shayen kayan maye.

Ya gargadi kungiyar musulmi ta Najeriya, MCN, a kan ta ci gaba da ayyuka nagari da ta saba kuma ta yi kokari wajen ladabtar da Zainab domin koma wa hanyar gaskiya.

Jami’i mai shigar da kara a gaban kotu, Ibrahim Shu’aibu, ya bayar da shaidar cewa jami’an tsaro na ‘yan sanda ne suka cafke Zainab a yayin da take tsaka da zukar tabar wiwi a kan titi.

Kamar yadda Shu’aibu ya bayyana a gaban kotu, an taba kama Zainab da laifi kuma ta yi zaman gidan Dan Kande a sanadiyyar gaza biyan kudin tara na N7,000 da aka shimfida a kanta har zuwa lokacin da kungiyar MCN ta fito da ita bayan ta biya tarar da ke wuyanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here