‘Yan Jarida Sun Hada Gwiwa Da Kungiyoyi Domin Bin Diddigin Alkawuran Da El-Rufa’i Ya Cika A Kaduna

0
375

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU ‘yan jaridu da kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) sun lashi takobin gudanar da binciken bin ‘kwakwafi’ a kan alkawuran yakin neman zabe da Gwamnan jihar Kaduna ya yi da kuma ci gaba da bin diddigin sabbin alkawuran da ya dauka a cikin jawabin da ya gabatar ranar rantsar da shi.

Kazalika, sun ce zasu ci gaba da bin kadin dukkan alkawuran yakin neman zabe da Gwamna El-Rufa’i ya dauka tare da bayyana cewa yin hakan zai sa gwamnati ta tashi tsaye haikan wajen ganin ta cika alkawuran da ta dauka.

‘Yan jaridun sun bayyana hakan ne ranar Alhamis a karshen wani taro da suka yi a garin Kaduna domin tattauna wa a kan alkawuran da gwamnan ya dauka yayin yakin neman zabe a jihar.

Daga cikin alkawuran da gwamna El-Rufa’i ya dauka akwai batun saka bukatar mutanen jihar Kaduna a farko, bayar da hutun watanni shidda ga mata ma’aikata bayan sun haihu, kaddamar da inshorar lafiya, samar da ababen more rayuwa domin inganta rayuwar jama’ar jihar Kaduna domin su kasance masu dogaro da kan su da sauran su.

Kazalika, El-Rufa’i ya dauki alkawarin samar da gidaje domin bawa jama’a damar mallakar muhalli na kashin kan su da kuma inganta makarantun firamare a fadin jihar.

Mahalarta taron sun yaba wa gwamnatin jihar Kaduna bisa kirkirar ma’aikatar kula da tsaron jiha da kuma kafa kwamitocin tabbatar da zaman lafiya a kananan hukumomin jihar.

Sun bayyana cewa bangaren yada labarai da kungiyoyi asu zaman kansu na da muhimmiyar rawar da za su iya taka wa wajen ganin cewa gwamnan ya cika alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here