An Saki Naziru Sarkin Waka Bayan Cika Sharudan Beli

1
723
Rabo Haladu Da Usman Nasidi, Daga Kaduna
WATA kotun majistre a Kano ta saki Nazir Ahmad Sarkin Waka, bayan ya cika sharudan belin da kotun ta yanka masa.
Da yammacin Juma’ar nan ne dai aka cika sharudan da kotun ta sanya masa a jiya Alhamis.
Sharudan sun kunshi ajiye N500,000 da samun manyan ma’aikatan gwamnati biyu da mai unguwa da za su tsaya masa, da kuma mika wa kotu fasfo din sa na tafiye-tafiye.
Bayanan da manema Labarai   su ka samu daga wasu na hannun daman Nazirun sun ce an sha matukar wuya kafin cimma wadannan sharuda.
A ranar Laraba ne ‘yan sandan suka kama Naziru a gidansa da ke Kano, bisa umarnin kotu, wacce ta samu korafi a kan mawakin.
Kotun ta sanya ranar 30 ga wannan watan na Satumba domin ci gaba da shari’ar.
‘Yan Kannywood sun yi raddi kan kama Naziru Sarkin Waka
Ana zargin Nazirun ne da sakin wani kundin wakoki ba tare da hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta sahhale masa ba.
Kamfanin Saira Movies ne dai ya saki wakokin, abin da ya sa wasu suke ganin cewa kamfanin na Saira ya kamata a tuhuma tunda shi ne ke da hakkin mallakar kundin.
A cikin shekarar nan ne Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nada Naziru a matsayin Sarkin Wakar sarkin Kano.
Nadin na sa ya zo ne a dai dai lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin Sarkin Kano da gwamnan Kano.
Wasu dai na ganin kamun na sa da tuhumar da aka yi masa na da dangantaka da siyasa.
To sai dai shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta Kano Ismail Na Abba Afakallah ya ce babu sisaya a cikin batun, an dauki matakin ne saboda ya saba ka’ida.
A baya dai Naziru da wani mawaki Ibrahim Ibrahim sun yi wa gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje wakar yabo ta ” A sha shayi”, lokacin da gwamnan ya rabawa masu sayar da shayi tallafi.
Daga baya kuma Nazirun ya koma yi wa bangaren Kwankwasiyya waka, abin da ke nuna sun raba tafiya da bangaren Gandujiyya.
A watan Agusta ma hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kama Sanusi Oscar bisa zargin sakin wata waka da za ta lalata tarbiyya, ba kuma tare da an tantance wakar ba.
‘Yan Kannywood da dama dai sun yi Allah wadai da kamun da ake yi wa mutane da ake gani suna da sabanin akidar siyasa da gwamnatin Kano.
Sai dai gwamnatin na musanta cewa akwai siyasa a lamarin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here