Manufar Buhari Game Da Najeriya Ta Banbanta Da Ta Osinbajo – Shehu Sani

  0
  827

  Usman Nasidi, Daga Kaduna.

  TSOHON Sanata kuma fitaccen mai fafutukar kare hakkin bil’adama a Najeriya, Sanata Shehu Sani ya ce Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo na da banbancin manufa game da Najeriya.

  Wannan zancen na Shehu Sanin a zuwa ne bayan da Shugaba Buhari ya ce mutum miliyan 100 za su fitar daga cikin halin talauci a shekara goma, yayin da shi kuma Osinbajo ya fadi cewa mutum miliyan 10 ne za a fitar a cikin shekaru goma.

  Da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan magana, tsohon sanatan ya ce akwai rudani tattare da jagorancin Najeriya ganin cewa kalaman shugaban kasa da mataimakinsa na cin karo da juna.

  A wani labari makamancin wannan zaku ji cewa, Shugaba Buhari ya bayyana abin da ya hana jininsa hawa dangane da shari’arsa da Atiku.

  Shugaban kasan ya ce taron majalisar zartarwa wato FEC wanda ya ci karo da lokacin shari’ar yayi matukar taimaka masa ta hanyar dauke hankalinsa daga shari’ar.

  Buhari ya fadin wannan maganar ne fadar Villa ranar Juma’a 13 ga watan Satumba lokacin da gwamnonin APC suka kai masa wata ziyara ta musamman.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here