Za Mu Kai Karar Masu Rubuta Labaran Karya A Kan Jiharmu Kotu – El-Rufa’i

0
349

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce rashin zaman mutum a Kaduna ba zai hana a tasa keyarsa zuwa gaban kotu ba idan har yana yada labaran karya game da jihar.

El-Rufa’i ya fadi wannan maganar ne ranar Talata a Abuja wurin bikin wallafa wani littafi mai suna ‘Digital Wealth’ wanda Japheth Omojuwa ya rubuta.

A cewar Gwamnan, da asalin masu wallafa labaran a tuwita da kuma wadanda ke sake yadawa abin da ake cewa re-tweet za su jefa kansu cikin matsala idan har labarin ya yi sanadiyyar rasa rayuka ko kuma sanya mutane cikin rudani.

Hakazalika, ya kara da cewa ana iya amfani da shafukan sada zumunta domin yin abu mai amfani, haka kuma idan ba a yi amfani da shi ta hanyar da ya dace ba zai kawo aibu.

El-Rufa’i ya ce: “Kada mu hada ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma ‘yancin kisan rayuka, idan ka rubuta labarin karya zai iya sanadiyyar kashe-kashe da ba ka san adadinsu ba. A dalilin wannan akwai bukatar ka gurfana gaban kotu domin amsa jawabi a kan kashe-kashen da ka haddasa.

“A jihar Kaduna, mun dauki matakai tsaurara game da wannan abu. Saboda a sakamakon yada labaran karya a shafukan sadarwa na zamani mutane da dama sun rasa rayukansu.

“Hakan ne ya sa muka tashi tsaye a kan wannan mummunan aiki, babu yadda za a yi kana Legas ko Fatakwal ka rika ba da labarin abin da ke aukuwa a Kaduna. Za mu kai mutum gaban alkali domin a zartar masa da hukunci. ” A cewar El-Rufa’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here