Akwai Tatsunniya A Batun Tashar Mambila – Minista

0
654
Mustapha Imrana Abdullahi
AN bayyana batun aikin samar da tashar hasken wutar lantarki ta Mambila da cewa akwai tatsunniya a cikin lamarin.

Sabon ministan ma’aikatar samar da hasken wutar lantarki Na tarayyar Nijeriya Injiniya Sale Hassan ne ya bayyana hakan a hirarsa da Gidan rediyon BBC Mai yada shirinsa a harshen hausa.
Injiniya Sale Hassan ya bayyana cewa a gaskiya domin Allah sabanin irin yadda ake yada lamarin cewa wai har an kusa kammala tashar abin ba haka yake ba.
“Akwai siyasa mai karfi a lamarin da har wadanda ba sa son a yi wannan aikin suka mayar da lamarin fitina, Amma a yanzu komai ya kawo karshe za a yi aikin cikin hukuncin Allah kasancewar an shiga yarjejeniya mai karfi da Turawan Jamus kuma su kawai ake jira domin fara aikin.
Ministan ya go gaba da cewa kasancewar tsakaninsa da Gwamnan Jihar Taraba akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu a yanzu tuni har Gwamnan ya sa hannun amincewa a fara aikin sabanin da can baya inda ko sa hannun amincewar ba a samu ba daga Gwamnatin Jihar.
“A can baya an cinye makudan kudi a kan cewar za a yi aikin amma ko filin wurin ba a je ba aka cinye kudi duk da yawansu, amma yanzu lamarin ba haka yake ba aikin zai kankama nan da dan lokaci kadan”.
Ba batun shekara daya ko biyu ba ne saboda aikin na cin kudi makudai kuma da lokaci, amma aikin za a yi shi ba wata tantama.
Ya kara da cewa za a biya diyya kadan kadan ga  masu wuraren da za a share a fara aikin domin za a gina har filin jirgin sama kafin fara aikin tare nan a gina nan kamar sai yadda aka san aikin da shi.
Game da batun kamfanonin da suke sayen wutar lantarki daga gwamnatin tarayya suna sayar wa da jama’a da kamfanoni kuwa Minista Sale Hassan, ya tabbatar wa da jama’a cewa za su zauna da duk kamfanonin domin jin ko za su iya ci gaba da harkar.
Ya kuma bada misali da wani kamfanonin da yake a Yola inda a yanzu suka ce sun fasa don ba za su iya ci gaba da harkar sayen wutar lantarkin ba suna sayarwa, kuma tuni suka yi tafiyarsu.
“Ba zai yuwu ba Gwamnatin ta ci gaba da zuba Kudi a lamarin amma su kamfanonin ba su iya cika nasu alkawarin ba, kasancewar tun can baya an yi yarjejeniyar kowa ga aikin da zai yi gwamnati ga na ta su kuma kamfanonin da ke sayen wutar ga nasu bangaren”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here