Kayan Sojoji Muke Karba Haya Idan Za Mu Fita Aiki – Mai Garkuwa Da Mutane

0
429

Daga Usman Nasidi.

DAYA daga cikin wasu ‘yan ta’adda uku da jami’an tsaro tare da hadin gwiwar kungiyar Fulani makiyaya (Miyetti Allah) suka kama a jihar Kano ya bayyana cewa suna amfani da kakin sojoji na gaske wajen gudanar da aikinsu.

Sai da jami’an ‘yan sanda na atisayen ‘Puff Adder’ da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da wakilan kungiyar Miyetti Allah ne suka hada gwiwa kafin kama ‘yan ta’addar uku; Lawan Mohammed, Sulaiman Abdullahi da Sai’du Abdullahi.

Jami’an tsaron na zargin Lawan da Sulaiman da laifin satar shanu, yayin da shi kuma Sa’idu ake zarginsa da laifin satar mutane domin yin garkuwa da su. A yayin baje kolin masu laifin ne Sa’idu ya bayyana cewa da kayan sojoji yake amfani duk lokacin da za su fita aiki.

An samu shanun sata fiye da 1,000 bayan jami’an tsaron na hadin gwiwa sun samu nasarar cafke masu laifin a Kano.

Kazalika, an samu bindigu, alburusai da wasu kayan sojoji bayan an cafke mai garkuwa da mutane, Sai’idu.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa shugabanninsu ne ke karbo musu hayar kayan sojoji kuma su mayar da kayan ga sojojin bayan sun kammala amfani da su. Sai dai, ya ce bai taba haduwa da jami’an sojojin da ake karbo kakinsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here