An Karrama Shugaban Kwalejin Al’ummar Musulmi Ta Funtuwa

0
526
Mustapha Imrana Abdullah
SAKAMAKON aiki tukuru tare da kishin al’ummar kasa baki daya ya sa kamfanin Jaridar Taskira da ke da babban mazauninta a garin Zariya ta karrama Alhaji Umar Aminu Imam da lamba mai nuna cewa shi ne gwarzon shugaba a jerin irin wadannan shugabannin kwalejin koyar da harkokin kiwon lafiya.
Kamar dai yadda tarihin makarantar ya nuna cewa dalibai Musulmi ne suka fara assasa makarantar ta yadda suke horar da jama’a aikin unguwar zoma domin kula wa da mata masu ciki da kuma karbar haihuwa a yankunan karkara ta yadda al’umma za su amfana.
Bisa bin wannan tsarin ne a halin yanzu a duk daukacin arewacin Nijeriya babu makarantar da ke gaban kwalejin a wajen koyar da al’amuran lafiya wanda hakan ya ba Musulmi wani babban tagomashi a duk fadin duniya.
Kamar yadda hukumar kula da makarantu irin wadannan suke tabbatar da cewa makarantar da Umar Aminu Imam ke wa jagoranci da ke da mazauninta a garin funtuwa ita ce kan gaba a tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanunsa cewa makarantar na da ingantattun na’urorin zamani domin koyar da dalibai, irin abin da ba kasafai ake samunsa ba a makarantu irin na “Musulim community college of health science an technology Funtua”.
Makarantar dai na da dalibai da suka fito daga kusan dukkan Jihohin Nijeriya da yawansu a halin yanzu ya wuce dubu uku

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here