Gwamna Lalong Ya Bai Wa Sakataren ‘Yan Agajin Izala Kwamishina

0
563

 Isah Ahmed Daga  Jos

SAKATAREN ‘yan agajin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Malam Muhammad Muhammad Abubakar yana daya daga cikin sunayen sababbin  kwamishinoni guda 23 da Gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya gabatar wa majalisar dokoki ta jihar Filato domin tantancewa.

Sunayen sababbin kwamishinonin ya nuna cewa akwai sunayen tsofaffin kwamishinoni 11 da aka sake dawo da su. A yayinda aka kawo sababbin sunayen kwamishinonin  12.

Da yake karantawa ‘yan majalisar dokokin  sunayen sababbin kwamishinonin a ranar Talatar nan da ta gabata, shugaban majalisar Honarabul Ayuba Abok ya bayyana cewa sunayen tsofaffin kwamishinonin 11 da aka sake dawo da su, sun hada da  Alhaji Dayyabu Garga da Yakubu Dati da Mista Dan Manjang da Idi Usman Bamayi da Victor Lapang da Regina Soemlat da Tamwakat Weli da Sylvester Wallangko da Elizabeth Wapmuk da  Dakur Jude Eli da kuma Pam Botmang.

Sunayen sababbin kwamishinonin 12 da aka gabatar sun hada da Chrisantus Ahmadu da Muhammad Muhammad Abubakar da Jerry Werr da Sambo Rebecca Adar da Abe Aku da Dung Musa Gyang da Tapgun Sylvanus da Nimkong Lar-Ndam da Kak ‘Mena Goteng Audu da Ibrahim Saad Bello da Rimven Bitrus  Zulfa da kuma Hosea Istifanus Finangwai.

Majalisar ta sanya ranar 23 ga wannan wata a matsayin ranar da za ta fara tantance sunayen wadannan kwamishinoni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here