NECO Za Ta Saki Sakamakon Jarrabawar Dalibai 30,000 Muddin Gwamnatin Neja Ta Biya Naira Miliyan 200

0
465

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Neja ta ce ta biya hukumar jarrabawar NECO naira miliyan 200, domin tabbatar da ganin an saki sakamakon jarrabawar dalibai 30,000 wanda hukumar ta rike.

A wani jawabin daga Mary Barje, Babbar Sakatariyar sadarwa ta Gwamna Abubakar Bello ta bayyana a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, cewa kudin ya kasance wani bangare na kudin jarrabawar da hukumar ke bin jihar.

Ta bayyana cewa gwamnatin ta biya fiye da Naira Biliyan daya zuwa ga hukumomin jarrabawa daban-daban cikin shekaru uku da suka gabata, duk cikin kokarin samar da ilimin boko kyauta ga dalibai a jihar.

Jawabin ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince za ta biya hukumar jarrabawar Naira Miliyan 50 a kowane wata, don sauke bashin da ke kasa.

Ta ce “Gwamnatin ta sadu da jami’an NECO; mun yi yarjejeniya, bayan mun biya wasu kudade cikin makon da ya gabata, hukumar ta yi alkawatin sake sakamakon daliban.”

Jawabin ya bayyana jajircewar gwamnatin da kuma kokarinta wajen bunkasa fannin ilimi, inda ta kara da cewa fannin yana da muhimmanci kwarai da gaske a gwamnatin da Bello ke jagora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here