Wata Mata Ta Watsa Wa Yaro Dan Wata 10 Ruwan Zafi

0
396

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WATA kotun Majistare da ke zama a Zariya, jihar Kaduna, ta tsare wata matar aure, Nnennaya Edmond, a gidan yari kan zargin watsa wa wata mata mai goyo da danta mai watanni 10 ruwan zafi.

Matar na fuskantar tuhume-tuhume biyu na aikata laifi da haddasa rauni a jikin Gloria Cyril da danta mai watanni 10, Bright Cyril.

Rahotanni sun bayyana cewa daga mai laifin har mai karan na zama ne a gida guda a yankin cocin ECWA da ke Wusasa, Zariya, jihar Kaduna.

Mai shari’a, Abubakar Aliyu-Lamido, ya yi umurnin cewa a tsare mai laifin a gidan yari sannan ya dage zaman zuwa ranar 15 ga watan Oktoba, domin mai karar ta gabatar da shaidu.

Tun da farko dai, dan sanda mai kara, Sufeto Mannir Nasir, ya fada ma kotu cewa a ranar 10 ga watan Satumba, da misalin karfe 1:00 na dare, wata Mary Ijeoma ta kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda da ke Dan magaji.

Ya bayyana cewa Ijeoma ta zargi wacce ake kara da zuba wa yarta Gloria da jikanta mai watanni 10, Bright ruwan zafi.

Dan sandan ya kara d cewa wacce ke karar ta yi bayanin cewa hakan ya haddasa rauni a jikin uwar da danta inda aka yi gaggawar kai su asibitin St Luke, Wusasa, domin jinya.

Ya bayyana cewa laifin ya saba wa sashi na 223 da 216 na dokar 2017.

Sai dai wacce ake zargin ba ta amsa laifin tuhumar da ake yi mata ba.

Daga nan sai dan sanda, ya nemi kotu ta dan dage karar na dan gajeren lokaci domin ya gabatar da shaidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here