Majalisar Kasa Na Da Ja Kan Sabuwar dokar CBN Ta Ajiyar Kudade a Bankuna

0
300
Rabo Haladu Daga Kaduna
BABBAN bankin kasa wato CBN,a jiya Laraba ne ya sanar da cewa, bankunan kasuwanci irin su First Bank da GTBank da Zanith Bank da makamantansu za su fara cazar kwastomomin su adadin wani kaso daga cikin kuɗin da za su ajiye ko kuma za su fitar daga asusunsu, matuƙar dai wannan kuɗi ya kai N500,000 (dubu 500) ga kwastoma ɗaya, ko kuma N3,000,000 (miliyan 3) ga kamfanunnuka da manyan ma’aikatu.
Yadda tsarin yake, idan kaje da niyyar saka N500,000 a cikin asusun ka dole ne bankin zai cajeka kaso 3 na adadin wannan kuɗin, wanda wannan kaso ukun shi ne ya kama N15,000 (dubu 15). Kenan maimakon a baka N500,000 idan kazo cira, sai dai a baka N485,000. Amma idan kana da ragowar kuɗi a asusun sai a cira a cikin su a baka kuɗinka cikakke. Idan kuma ya kasance sanyawa kazo yi a cikin asusun ka bankin zai cajeka kaso 2 na wannan kuɗin, wanda ya kama N10,000. Kenan anan ma ba N500,000 za a sanya maka ba, N490,000 za a sanya maka.
Ga kamfanunnuka da manyan ma’aikatu kuwa, a duk N3,000,000 (miliyan 3) da za su sanya a asusun su banki zai ciri kaso 5, wanda ya kama N150,000 (dubu 100 da 50). Idan kuma cirewa za suyi, bankin zai ciri kaso 3, wanda shi ma ya kama N90,000 (dubu 90).
Kuma wannan dokar za ta fara ne a Jahohi 6 kawai, kafin daga bisani zuwa watan Maris ɗin shekarar 2020 tsarin ya karaɗe dukkan jahohin Ƙasar.
Jahohin su ne; Lagos da Ogun da Kano da Abia da Anambra da kuma Ribas Sai dai ‘ya’yan majalisar tarayya da majalisar dattijai sun fara zama kan wannan batu, inda suka yi tsayin daka suka yi kyememe don ganin ba su amince da kafa wannan dokar ta babban bankin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here