Gwamnatin Bauci Za Ta Samar Da Gidaje 2,500

0
416
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an sama wa jama’a musamman talakawa saukin wahalar gidajen da suke fama da shi a sako da lungunan Jihar Bauci ya sa Sanata Bala Muhammad Kauran Bauci ya nemo kamfanin da zai gina ingantattun gidaje a jihar.
A wajen wani kwarya-kwarya taron da aka yi tare da jami’an kamfanin gina gidaje da kuma gwamnatin jihar domin yarjejeniyar fara aikin a yankunan masarautun da ake da su a jihar, gwamnatin karkashin Bala Muhammad tare da kamfanin duk sun sha alwashin kammala aikin a cikin lokaci.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Gwamnan Bauci mai gayya mai aiki ya yi alkawarin ci gaba da sama wa mutane Bauci abubuwan more rayuwa kamar yadda ya dauki alkawarin zai yi.
Al’ummar jihar Bauci dai na nuna farin ciki da jin dadin wannan yarjejeniyar samar da gidaje dubu biyu da dari biyar abin da wani Auwal Mamman Kashere ya bayyana da ci gaban da suke tsammanin a samu wanda dalilin haka suka fito zabe.
Shi ma Abdulfatah Abba, cewa ya yi hakika irin wannan hangen nesa da kuma aiki tukuru ne Jihar Bauci ta dade da neman wanda zai dorata a kai don haka Alhamdulillahi tun da an samu mafita a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here