Mun Bukaci Dakatar Da Harajin CBN – ‘Yan Majalisa

0
341

MAJALISAR wakilan tarayyar Najeriya ta bukaci Babban Bankin Najeriya ya dakatar da umarnin da ya bai wa bankuna su karbi kashi biyu zuwa biyar a cikin 100 na tsabar kudin da ‘yan kasar suka shigar ko suka fitar daga asusun ajiya.

Matakin dai ya bukaci cire kason a kan duk garin kudin da aka fitar ko shigar matukar sun kai naira dubu 500 ga daidaikun mutane da kuma naira miliyan uku ga kamfanoni.

Majalisar yayin zamanta na ranar Alhamis, ta kafa kwamitin da zai yi nazari kan hanya mafi dacewar aiwatar da manufar.

Shugaban masu rinjaye a majalisar Alhassan Ado Doguwa ya shaida wa GTK cewa matakin da Babban Bankin Najeriya ya dauka masu kanana da matsakaitan masana’antu zai fi shafa.

Ya kara da cewa daman tun lokacin mulkin tsohon shugaban bankin Mai martaba sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi na biyu aka fito da tsarin, to amma tsarin na yanzu ya sha banban da na baya.

”Idan aka ce wannan haraji za a dora wa ‘yan kasuwa da ke yankunan karkara na ba gaira ba dalili bai dace ba. Mutane sun je sun ci kasuwar kauyuka, sai kuma a ce idan sun kai kudi banki za a dora musu wannan haraji ai babu adalci a nan”, in ji Alhassan Doguwa.

Majalisar wakilan za ta jira sakamakon binciken kwamitin, kafin daga bisani su dauki matakin da ya dace. A yanzu dai sun bukaci Babban Bankin Najeriya CBN ya dakatar da wannan mataki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here