An Nemi Wata Babbar Kwamandar Sojin Ruwa An Rasa A Jihar Kaduna

0
460

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

RAHOTANNI sun kawo cewa Kwamandar makarantar sakandare na ma’aikatan rundunar soji da ke Jaji, jihar Kaduna, O.O, Ogundana ta bata. Tsawon kwanaki hudu kenan ba a ga jami’ar rundunar sojn ruwan ba.

Rahotan daga wasu majiyoyin soji abin dogaro cewa yana iya yiwuwa kwamandar sojin ruwan ta bata tun kafin a ankara a ranar Litinin.

A cewar majiyoyin, gani na karshe da aka yi wa Misis Ogundana, mai lamban aiki NN/2367, ya kasance a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba.

Rashin zuwanta aiki a karshen makon ne ya sa aka fara zargin ko wani abu ya faru bayan ba ta hallara ba a ranar Litinin.

Majiyar ta ce lokacin da aka je aka duba gidanta mai lamba 22, AVM a Crescent ne aka tabbatar da cewar ta bata.

Majiyoyin sun ce an fasa kofar gidan a lokacin da aka ji wayanta na kara a cikin falonta.

Sun kuma bayyana cewa duk wani kokari da aka yi domin samun layinta na Glo da Airtel ya ci tura.

An kuma lura cewa motarta, kirar Toyota Highlander kalar ruwan toka mai rijista da lambar Legas AAA 434 CF, ma ba ta nan .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here