Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Kaddamar Da Tsarin Takaita Amfani Da Takardun Naira – CBN

0
434

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN babban bankin Najeriya a ranar Juma’a ya ce bankin za ta ci gaba da kaddamar da shirin takaita amfani da kudin takarda wato ‘cashless policy’ a yunkurin da take yi na inganta hada-hadar kudi.

Gwamnan bankin, Mista Godwin Emefiele ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin tsare-tsare na kudi.

Ya karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa tsarin zai kuntata wa ‘yan Najeriya inda ya ce kimamin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na masu asusun bankuna ne abin zai shafa.

Ya ce muddin ana son tattalin arzikin Najeriya ya inganta kamar na kasashen da suka ci gaba,ya zama dole a rungumi tsarin yin kasuwanci ba tare da amfani da kudin takarda ba wurin hada-hadar.

Idan ba a manta ba, a baya majiyarmu ta ruwaito cewa majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeria wato CBN da ya dakatar da sabon tsarin da ya gabatar na takaita tu’amulli da tsabar naira tare da zare wani kaso cikin kudin masu ajiya idan za su cire tsabar kudi sama da N500,000.

A zaman majalisa na ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, majalisar dokokin ta ce manufar zai yi sanadiyyar samun gagarumin ragi a wajen tsawaita ba da rance a bankunan ajiya na Najeriya.

‘Yan majalisar sun kuma bayyana cewa tsarin zai kawo koma-baya kan masu kanana da matsakaitan kasuwanci “wanda su ne ginshikin habbakan tattalin arziki.”

Sai babban bankin na kasa ya ce ba rashin fahimtar abin da tsarin ya kunsa ne ya sa wasu daga cikin al’umma ba su yi maraba da shi da farko ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here