Gwamnonin PDP 7 Sun Yi Taron Sirri A Fatakwal

  0
  706
  Mustapha Imrana Abdullahi
  GWAMNONIN da suka ci zabe karkashin jam’iyyar PDP gidaje shida sun yi taro da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Ezenwo Wike a garin Fatakwal.
  Taron dai an yi shi ne a daren jiya Juma’a a gidan gwamnati da ke Fatakwal.
  Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Ribas na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai da suka shafi rediyo da makamantan su Mustapha Simeon Nwakaudu ne ya fadi haka tare da sanarwar yin taron.
  Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Adamawa Umaru Fintiri, Imo , Emeka Ihedioha, Oyo , Seyi Makinde, Benue  Samuel Ortom, Sakkwato Amimu Waziri Tambuwal da Zamfara Bello Mohammed Mattawale.
  Gwamnonin sun isa gidan gwamnatin Jihar Ribas ne da misalin karfe shida na yamma sai suka tafi gidan Gwamna Wike inda suka yi taron cikin sirri tare da Gwamnan na Ribas.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here