Wata Kotun Tarayya Ta Yanke Hukuncin Anshe kaddarorin Kamfanin P&ID

0
339
Rabo Haladu Daga Kaduna
 WATA kotun tarraiya ta yanke hukuncin amshe kaddarorin da kamfanin P&ID ke da shi, a matsayin hukuncin laifuka yadda dokar kasa ta tanada, kamar yadda hukumar yaki da rashawa da bin diddigin yi wa kasa ta’annati wato EFCC ta yi.
Bayan wadanda ake zargi, Mohammed Kuchazi da Adamu Usman, wadanda su ne daraktocin kamfani sun amsa laifin su, alkalin kotun tarrayya Edward Ekwo, ya yanke hukuncin karbe kadarorin kamfanin P&ID a matsayin hukuncin laifuka kamar yadda doka ta tanada, kuma kotu ta ce za a mika wa gwamnatin Najeriya kaddarorin.
Laifukan da ake zargin su da aikata wa, sun hada da almundahanar kudade,,da yin amfani da ofishinsu ba yadda ya kamata ba, da kuma yi wa kasa zagon kasa.
An kama Mohammed Kuchazi da laifuka 10, shi kuma Adamu Usman an kama shi da laifuka 11.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kare, idan an mika wanan hukuncin ga kasar Ingila wace a gabanin wannan hukunci ta ci tarar Najeriya kudi Dalar Amurka Biliyan 9 da digo 6.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here