Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyar Rufe Wasu Makarantu A Jigawa

0
386
Rabo Haladu Daga Kaduna
AMBALIYAR ruwan sama ya yi sanadiyyar rufe wasu hanyoyi 4 da zai dangana dalibai zuwa makaranta a karamar hukumar Auyo da ke jihar Jigawa.
Sakataren ilimin na yankin Alhaji Ibrahim Dauda ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Dutse hedikwatar jihar Jigawa.
Alhaji Ibrahim Dauda ya ce daga cikin makarantun da abin ya shafa sun hada da karamar sakandire ta Unik-Babba da makarantar firamare ta Unik Gana da makarantar Sakandire ta Afarmo da kuma makarantar firamare ta Gayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here