A Farfado Da Ayyukan Kungiyoyin Aikin Gayya A Jihar Kano-Inji Shugaban Kwamitin Koli

0
474

JABIRU A HASSAN, Daga  Kano.

SHUGABAN kwamitin koli na kungiyoyin aiyukan gayya a jihar Kano Alhaji Ibrahim Garba Aminu Kofar Na’isa ya bukaci gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ta farfado da ayyukan kungiyoyin aikin gayya a jihar ta yadda shirin tsaftar muhalli zai cimma nasara.

Ya yi wannan bayani ne a hirarsu da wakilinmu a ofishin sa, inda ya nunar da cewa kungiyoyin aikin gayya suna taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gwamnati dangane da shirin tsaftace muhalli da samar  da ayyukan raya kasa kamar gyaran hanyoyi da magudadun ruwa da gina  kwalbatoci da  makarantu sauran aikace-aikace muhimmai ga al’uma.

Alhaji Ibrahim Garba  Aminu Kofar Na’isa ya yaba wa Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarinsa na tabbatar da tsaftar muhalli a fadin jihar Kano wanda hakan ta sanya ake cimma nasarar aiwatar da shirin nan na tsaftar muhalli na karshen wata, tare da yin kira ga Gwamna Ganduje da ya farfado da aikin gayya da samar da kayan aiki ga kungiyoyin ta yadda za’a ci  gaba da aiki domin gyaran muhalli.

A karshe, shugaban kwamitin kolin ya jaddada cewa za su ci gaba da kokari wajen hada kan yan kungiyoyin aikin gayya da ke jihar ta Kano tareda tabbatar da ganin cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu a duk lokacin da aka gabatar da aikin gayya na gamayyar kungiyoyin ayyukan gayya a cikin birnin Kano da kuma yankunan karkara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here