Matatun Man Fetur 3 Za Su Fara Tace Mai Daga Watan Janairu – NNPC

0
372

Daga Usman Nasidi.

MATATUN man fetur guda uku da ke Fatakwal, Warri da Kaduna za su fara aikin tace danyen man fetur gadan-gadan daga shekarar 2022, kamar yadda kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ya sanar a daren ranar Asabar.

Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai matatar man fetur da ke Fatakwal, ya bayyana cewar za a fara gyaran matatun man fetur din daga watan Janairu, 2020.

Wani jawabi da Ndu Ughamadu, jami’in hulda da jama’a na NNPC, ya fitar, ya ce ziyarar da Kyari ya kai matatar man na daga cikin kokarinsa na tabbatar da cewa matatun sun fara aiki cikin lokacin da NNPC ta tsara.

Kyari ya ce fara aikin matatun man na daga cikin manyan aiyukan da NNPC ta ba wa fifiko tare da bayyana cewa hukumar NNPC ba za ta bari wani abu ya dauke hankalinta daga ganin ta cimma wannan kudiri nata ba.

” Za mu yi aiki da lokaci, za mu tabbatar mun cimma muradin mu a shekarar 2022 kamar yadda muka dauki alkawari. Za mu fara aikin gyaran matatun a watan Janairu na shekarar 2020. Za mu samar da dukkan kayan aiki da ake bukata domin fara aikin a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba.

“Na tabbata hakan mai yiwuwa ne, saboda irin goyon bayan da muke da shi daga gwamnatin tarayya, masu ruwa da tsaki, ‘yan kwangila da kuma ma’ikatan NNPC. Ba ni da shakku a kan cewa zamu cimma muradinmu kuma a kan lokacin da muka tsara ,” a cewar Kyari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here