Ana Samun Sauyi Mai Ma’ana A Hukumar Ilimin Bai Daya Ta Jihar  Kano (SUBEB)

0
559
Gwamnan Jihar KANO Dakta Umar Abdullahi Ganduje

JABIRU A HASSAN, Daga  Kano.

AN bayyana cewa yanzu an fara samun sauyi a hukumar ilimin bai daya  ta jihar Kano wato SUBEB musamman ganin yadda wannan hukuma ta kula da makarantun firamare ta sami shugaba kwararre wajen jagorancin harkar ilimi da kyautata yanayin koyo da koyarwa a fadin  jihar Kano.

Sannan ko shakka babu, malamai da iyayem yara sun yaba da yadda sabon  shuhaban hukumar kula da makarantun firamare, Dokta Danlami Hayyo ya fara kafa wa hukumar ginshiki mai inganci domin  tafiyar da aikace-aikace ta yadda kwalliya zata ci  gaba da biyan kudin sabulu a wannan hukuma domin bunkasa ilimin firamare a jihar  Kano.

Haka kuma  bisa ga irin gogewa da kwarewa ta Dokta Danlami Hayyo yake  da ita  a fannin ilimi, babu shakka za’a sami ingantuwar al’amura a hukumar ta SUBEB musamman ganin cewa ilimin firamare shine ake samu daga  tushe gashi kuma gwamnatin jihar  Kano ta yunkuro wajen bada ilimi kuma ingantacce a matakin firamare da sakandire kyauta a fadin  jihar.

Mafiya yawan iyaye da malamai sun bayyana cewa ko shakka babu, Dokta Danlami Hayyo zai yi aiki mai gamsarwa wajen taimakawa kokarin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje  dangane da cimma  nasarar  shirin bada ilimi kyauta a jihar  ta Kano, tareda dora  shi kansa  ilimin na firamare kan ginshiki mai kyau.

Daga  karshe, ana bukatar ganin ana samun cikakken hadin  kai tsakanin shugaban hukumar ta SUBEB  Dokta Danlami Hayyo da sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 44 dake  fadin jihar  kano da shugabannin sassa na hukumar dake  aiki tare da shugaban da iyayen yara da malamai da kuma  shugabannin makarantun firamare watau Hesimastoci ta yadda aiki zai tafi  cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here