Honorabul Lere Ya Raba Wa Jama’a Motoci 20

0
613
Mustapha Imrana Abdullahi
DAN Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar al’ummar karamar hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Injiniya Suleiman Aliyu Lere da ake yi wa lakabi da Gari Ya Waye, ya raba wa jama’ar mazabarsa motoci ashirin domin su mori romon mulkin dimokuradiyya.
Suleiman Aliyu Lere ya raba wadannan motoci ne a wajen wani babban taron da suka yi a garin na Lere.
Taron dai ya samu halaryar shugabannin majalisar da suka hada da shugaban masu rinjaye Honarabul Alhassan Ado Doguwa wanda a wajen taron ya bayyana cewa hakika wannan Dan majalisar da ake yi wa lakabi da Gari Ya Waye daga farawa har ya iya aiwatar da abubuwan alheri, don haka wannan tagomashi su ‘yan majalisa suna farin ciki da shi.
“Wannan kujera babu wata tantama ta tabbata ga Suleiman Gari Ya Waye ba canji yana nan daram”.
Da wakilinmu ya ji ta bakin wadanda suka amfana sun bayyana farin ciki da wannan tsarin Dan majalisa Suleiman Aliyu Lere, tsarin da suka bayyana da ba kasafai ake samun Dan majalisa ya yi irin wannan ba a dan kankanin lokaci da zuwa majalisa.
Don haka sun bayyana cikakken goyon baya da hadin kai ga Dan majalisa Suleiman Aliyu Lere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here