Kasuwar Garin Kankara Na Kara Bunkasa

  0
  736
  Na Duke Tsohon Ciniki Kowa Ya Zo Duniya Kai Ya Taras
  Mustapha Imrana Abdullahi
  TUN bayan da aka samu matsalar rashin tsarin da ta haifar wa da fataken da suke harkar saye da sayar da kayan kamfanin gona a yau Talata KASUWAR KANKARA da samu samar dawowa cikin matsayi ta na da inda suke amsar Fataken hatsi daga ko ina a ciki da wajen Nijeriya ga dai yadda farashin kayan hatsin yake kamar yadda wani sakatare a cikin shugabannin kasuwar Malam Sanusi Sadauki ya shaida wa majiyarmu lokacin da suka ziyarci kasuwar da ake sayar da Dawa, Masara, Waken Suwa (Jan wake), Farin wake, Gero, Gyada da sauran kayan da ake nomawa irin su Auduga da sauran su.
  1. SABUWAR MASARA BUHU MAI CIN TIYA 40 – N6,000-N7,000
  2. TSUHUWAR MASARA  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N8,500 – N9,000
  3. JAN WAKE (WAKEN SUYA)  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N10,000
  4. FARIN WAKE  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N15,000 – N15,500
  5. GERO  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N7,500 – N8,000
  6. SABUWAR GYADA  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N3,500
  7. DAWA  BUHU MAI CIN TIYA 40 – N5,000 – N5,500
  Wannan farashin na iya hawa ko ya sauka kafin kasuwar ta tashi.
  Addu’armu dai ita ce Allah ya karo mana zaman lafiya, ya sanya albarka ga nomanmu da kasuwarmu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here