Shin Birnin Kano Ta Dabo Mafakar Masu Aikata Miyagun Laifuffuka Ce?

0
476

MASU yabon birnin da kuma masu sukar sa na cewa birnin Kano ya yi fice wajen abubuwan alheri da akasin haka.

Ta ko wane bangare a iya cewa lamarin haka yake, duba da abubuwan arzikin da alkhairi da birnin ya tattara.

Haka kuma a daya bangaren, babu shakka birnin Kano ya shahara wajen wasu miyagun halaye da kuma wasu matsaloli da suka yi wa birnin katutu, ciki har da zama matattara ko mafakar miyagun mutane.

A ‘yan watannin nan, sunan Kano ya kara shiga bakin mutane, bayan da aka rinka kama wasu mutane da ake zargi da wasu manyan laifuka akai-akai.

A Kano ne aka kama shahararren wanda ake zargi din nan da satar mutane don neman kudin fansa da safarar makamai Hamisu Wadume, bayan an zargi wasu sojoji da kubutar da shi daga kwararrun ‘yan sandan da suka kama shi a jihar Taraba.

‘Yan kwanaki kadan bayan nan, aka kama jagoran gungun wasu ‘yan fashi da suka tare tawagar mataimakin gwamnan jihar Nasarawa a arewa maso tsakiyar Najeriya, inda har suka kashe ‘yan sanda biyu da ke yi masa rakiya.

An kama mutumin da ake zargin ne a unguwar Rijiyar Zaki da ke yammacin birnin Kano. An kuma samu bindigogi a gidan.

A watan Yulin 2019 kuma, an kubutar da Magajin Garin Daura a Kano bayan da wasu masu garkuwa da mutane suka dauke shi a gidansa da ke garin Daura a jihar Katsina, bayan ya shafe sama da wata guda a hannun mutanen da suka yi garkuwar da shi.

A tsakiyar watan Agustan 2019 ma, ‘yan sanda a Kano sun ce sun kama ‘yan fashi takwas da masu garkuwa da mutane 16 a birnin na Kano.

Lokacin da ake tsaka da matsalar Boko Haram a Kano a baya, birnin ya kasance wajen da manyan ‘yan Boko Haram suke samun mafaka.

Sau biyu Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yana tsallake rijiya da baya a Kano.

A lokuta daban-daban, jami’an tsaro sun samu labarin cewa Shekau yana Kano. Sai dai a duka lokatun ba su yi nasara ba a yunkurin da suka yi na kama shi.

Haka kuma a Kano ne aka kama shararren mai magana da yawun Boko Haram Abu Qaqa, ko da yake wasu bayanan na cewa kashe shi jam’ian tsaro suka yi a Kano a kan titin Maiduguri yana gab da shiga birnin na Kano.

Wasu masana al’amuran tsaro na cewa akwai ma wasu gaggan masu aikata laifuka a Najeriya da suke shiga Kano suna fita a lokuta daban-daban, ba tare da hukumomi sun kai ga kama su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here