Ta Karrama Wasu Muhimman Mutanen Yankin Saminaka

0
585
Darakta Janar na Hukumar samar da ruwa ta Jihar Kaduna Injiniya Manur Ahmed da Babban Sakatare a ma'aikatar ayyuka ta Jihar Kaduna Alhaji Bashir Umar Lere a wajen taron

Isah  Ahmed Daga Jos

 KUNGIYAR nan ta Saminaka Progresive Forum da ke Jihar Kaduna,  ta shirya wani  gagarumin taron karrama wasu mutanen yankin guda 5, da aka nada  a mukamai daban daban, a karshen makon da ya gabata.

Mutanen da aka karrama din, sun hada da Darakta Janar na hukumar samar da ruwa ta Jihar Kaduna, Injiniya Ahmed Manur  da Babban sakatare a ma’aikatar ayyuka ta Jihar Kaduna, Alhaji Bashir Umar Lere  da Mataimakin kwantirola Janar na hukumar gidajen yari ta Najeriya, Alhaji Rabi’u Babangida  da shugaban hukumar ilmin bai daya ta Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Sani, da kuma shugaban kwalejin koyan aikin gona ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya Dokta Abdullahi Namakka.

Da yake jawabi a wajen taron babban bako mai jawabi, kuma  Malami a sashin bincike da koyar da dabarun noma na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Salihu Dadari ya yi  kira ga al’umma su rika  kafa irin wadannan kungiyoyi, domin su rika yin abubuwan da za su kawo cigaba a yankunansu.

 Ya ce ya kamata ‘yan kasuwa da attajirai da ‘yan boko da manoma da ‘yan siyasa na yankin Karamar Hukumar Lere, da kasar nan baki daya  su  rika yin abubuwan da za su taimaki al’ummominsu.

Ya ce babu shakka ta hanyar  kafa irin wadannan kungiyoyi ne za a sami damar da za a rika baiwa dalibai tallafin karatu da tallafa wa harkokin  kiwon lafiya da  kuma tallafawa  wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.

Ya yi kira ga wadannan da aka karrama  su tallafa wa al’ummar wannan yanki, ta hanyar samarwa matasa ayyukan yi da kawo abubuwan da za su kawo ci gaba a yankin.

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar ta Saminaka Progresive Forum Alhaji Nuradeen  Danladi Salihu ya bayyana cewa wannan kungiya, ta kunshi ‘yan kasuwa da manoma da malaman addini da masu ilmin zamani da ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa.

Ya ce sun kafa  kungiyar  ne domin hada kan al’ummar  yankin, ganin cewa babu  al’ummar da za ta sami ci gaba ba tare da hadin kai ba.

‘’Duk wanda ya yi wani abun azo a gani na taimakawa al’umma a wannan yanki, za mu karrama shi. Domin babban burinmu shi ne ciyar da al’ummar wannan yanki gaba’’.

Alhaji Nuradeen ya yi bayanin cewa  kungiyar ta tallafawa daliban wannan yanki  da dama wajen shiga manyan makarantu da tallafawa jami’an tsaro da   gina gadar da ta hada cikin garin Saminaka da tasha.

A nasa jawabin a madadin wadanda aka karrama, Shugaban Hukumar Ilmin bai daya  ta Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Sani ya yaba wa kungiyar kan wannan karrama da aka yi masu. Ya yi  kira ga iyayen yara su rika  kokari suna  sanya yaransu  a makaranta.

Ya ce Hukumar ilmin bai daya ta Jihar Kaduna  tare da hadin gwiwar Hukumar kidayar al’umma ta kasa sun yi wani bincike, a inda suka gano cewa a Jihar Kaduna akwai yara sama da dubu 7 da basa zuwa makaranta.

‘’Don haka  hukumar ilmin bai daya ta Jihar Kaduna ta kudiri aniyar ganin ta komar da yara 145,000,00  makaranta a wannan shekara. Yanzu rayuwa ta canza domin  mutum ba zai iya yin wani abu ba, dole  sai da ilmi’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here