Ta Kashe Kanta Dalilin An Yi Mata Fada Kan Zagin Mahaifiyarta  

0
567
Marigayiya Fatima Jibrin

Isah  Ahmed Daga  Jos

WATA Bazawara ‘yar shekara 26 da haihuwa, mai suna Fatima Jibrin da aka fi sani da Talatuwa da take zaune a garin Lere, da ke karamar hukumar Lere a Jihar Kaduna, ta sha maganin kashe kwari na fiya fiya ta mutu. Saboda wani yayanta ya yi mata fada, kan zagin mahaifiyarta da take yi. Wannan al’amari ya faru ne a garin na Lere,  a karshen makon da ya gabata.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani, kan yadda wannan al’amari ya faru wani yayan marigayiyar, mai suna Lawal Aliyu Lere ya bayyana cewa gaskiyar magana, wannan yarinya ta kasance mara jin magana, kuma duk abin da ‘yan uwanta suke yi suna kokari ne su jawo hankalinta kan ta kasance tagari.

Ya ce ita dai wannan yarinya  a duniya babu wanda take so ta ci wa mutumci, sai mahaifiiyarta.

‘’Kuma abin da ya faru har ya kai ga wannan al’amari, ana yi mata fada ne kan ta bi  mahaifiyarta domin mahaifiyarta ba a  bar wulakantawa ba ce a gareta. Shi ne  wani yayanmu ya ce duk ranar da yaji, ta sake cin mutuncin mahaifiyarta,  zai yi mata duka’’.

Lawal Aliyu ya yi bayanin cewa da marigayar ta ji yayan namu ya ce haka, sai ta ce tun da an ki jininta za ta tafi kogi, ta fada ruwa ta mutu.

Ya ce daga nan da ta fita daga gida ba a sani ba, sai taje ta sayi fiya fiya a wani shago da ke kusa da gidansu ta sha. Bayan ta dade da shan wannan magani, sai take fada wa mutane cewa ta sha fiya fiya.

Ya  ce kafin a kawo mata dauki, a kai ta asibiti maganin fiya fiyan ya ci karfinta, don haka nan  ta rasu a gida.

Ya ce bayan faruwar wannan al’amari, babu wani mataki da suka dauka, saboda ita ce da kanta ta yi wannan abu. Don haka aka shirya aka yi mata jana’iza, aka yi mata addu’o’in Allah ya gabafarta mata. Ya ce gaskiya ba su ji dadin faruwar wannan al’amari ba.

Ya ce marigayiyar ta yi aure har ta haifi yara 2 amma auren ya mutu shekaru 2 da suka gabata, don haka take zaune a gida tana zawarci.

Wakilinmu ya tuntubi Magajin garin Lere Alhaji Yakubu Sulaiman Lere kan wannan al’amari, domin jin ta bakinsa inda ya bayyana cewa gaskiya ba su ji dadin faruwar wannan al’amari ba. Domin wannan abu da marigayiyar ta aikata na kashe kanta, kamar kafirci ne. Ya ce ba a taba samun faruwar irin wannan al’amari ba, a wannan gari.

Ya yi kira ga matasa maza da mata   su rika bin maganar iyayensu, domin su rabu da iyayensu lafiya kuma su gama da duniya lafiya.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo kan wannan al’amari  ta waya,  amma bai same shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here