‘Ya’yan APC Na Gwandu Sun Amince Da Injiniya Bello Kurya

  0
  785
  Mustapha Imrana Abdullahi
  SHUGABANNIN  jam’iyyar APC baki daya tare da jagororinsu na karamar hukumar Gwandu sun sa kiran uwar jam’iyyar ta jiha inda duk suka amince da Injiniya Bello Kurya a matsayin dan takardar shugaban karamar hukumar Gwandu.
  Alhaji Mamuda A Mode, shugaban jam’iyyar APC a matakin karamar hukumar ya bayyana farin cikinsa da wannan kokarin amincewa da bukatar jam’iyyar a kan batun Injiniya Bello Kurya, a matsayin dan takarar APC na karamar hukumar Gwandu.
  Daya daga cikin ‘yan takarar goma sha hudu Honarabul Abubakar Aliyu Warari,ya bayyana farin cikinsa bisa wannan hadin kai da aka samu a tsakaninsu na amincewa da Injiniya  Bello Kurya, a matsayin dan takararsu.
  Shima da yake nashi Jawabin Honarabul  Atiku Ahmed Gwandu, da ake wa lakabi da  (Culture) ya bayyana matakai har guda uku da suka bi  kamin amincewa da Injiniya Bello Kurya, amatsayin dan takarar Jam’iyyar APC na karamar hukumar mulki ta Gwandu.
  Ga dai matsala kamar haka:
  1.Masu ruwa da tsaki sun yi la’akari da mazabun da ba su taba rike babban mukami ba mazabun sune Maruda,Malisa,Cheberu da Gulmare.
  2. Duk da haka sun sake la’akari da cewa mazabar Maruda ita ce ta yi dai dai da inda ya kamata su mu dan takarar karamar hukuma a Jam’iyyar apc da zai jagoranci karamar hukumar Gwandu.
  3. Masu ruwa da tsakin sun yi la’akari da kammaluwar sharuddan shugabancin na Injiniya  Bello Kurya.
  Bisa irin wadannan ne aka ga lallai Injiniya Bello Kurya ya dace da wannan takarar a matakin karamar hukuma.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here