An Bankado Wata Kitimurmura Da Ganduje Yake Shirya Wa Sarkin Kano

0
654

Daga Usman Nasidi.

DATTAWAN jahar Kano a karkashin kungiyar sake farfado da martabar jahar Kano sun bankado wata sabuwar kitimurmura da Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yake shiryawa na tsige mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Majiyarmu ta samu labarin cewa tun bayan da Gwaman jahar Kano ya kirkiri sabbin masarautu guda 4 a jahar Kano, tare da rage ma Sarki Sunusi karfin iko, aka lura Sarkin ya janye daga halartar tarukan gwamnatin jahar.

Ita kuwa gwamnatin jahar tuni ta zabi ta dinga mu’amala da sauran Sarakunan, musamman ma Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero. Da wannan ne majiyoyi na karkashin kasa suka tabbatar da cewa Gwamnan ya fara shirin mayar da Sarki Sunusi zuwa garin Bichi, tare da mayar da Sarki Aminu Ado zuwa Kano.

“Manuniya ta nuna Sarki Sunusi ba zai amince da sauya masa masarauta ba, don haka ba zai amshi sarautar Sarkin Bichi ba, don haka idan ya ki amincewa, sai su tuhume shi da rashin biyayya da wannan za su tsige shi.” Inji majiyar.

Majiyarmu ta samu labari daga wata majiya ta karkashin kasa da tace an sanar da fadar shugaban kasa halin da ake ciki domin ta shawo kan Gwamna Ganduje ya hakura, domin kuwa a yanzu haka Sarkin yana kasar Amurka inda ya halarci taron majalisar dinkin duniya tare da shugaba Buhari.

Cikin wata sanarwa da dattawan Kano suka fitar ta bakin Ibrahim Waiya a ranar Alhamis, sun bayyana cewa gwamnan ya kudurci daukan matakin ramuwar gayya fiye da ci gaban Kano.

“Mun samu labarin gwamnatin jahar Kano na shirin mayar da mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II zuwa masarautar Bichi, kuma idan ya ki su tsige shi, wannan abu bai yi dadi ba duba da cewa akwai hukuncin kotu da ta umarci a dakata da yin komai har sai ta yanke hukunci.

“Wannan ka iya janyo tashin hankali da rikici a jahar Kano, don haka zamu yi iya bakin kokarinmu domin mu ga mun tabbatar da zaman lafiya a jahar Kano ta hanyar kira ga gwamnatin tarayya da manyan mutane da su ja hankalin Gwamnan ya dakatar da muguwar manufar da yake da ita a kan Sarkin Sunusi II.” Inji shi.

Daga karshe kungiyar ta ce idan har Gwamnan bai ji kiraye kirayen jama’a ba, har ta kai ga ya tsige Sarkin, toh za su nemi gwamnatin tarayya ta kaddamar da dokar ta baci a jahar Kano domin kare jahar Kano da abin da ka iya biyo baya, kamar yadda ta auku a shekarar 1981 lokacin da aka yi kokarin tsige Ado Bayero

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here