Hukumar NDLEA A Kaduna Sun Yi Wawan Kamu

0
435
Mustapha Imrana Abdullahi
HUKUMAR hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin Kwamanda Bala Fage, sun yi gagarumin kamu na haramtattun kayan maye.
Daukacin wannan nasara da za ku iya ganin hoton a farkon wannan labarin kamar yadda rundunar ta shaidawa manema labarai sun yi shi ne a watan Satumba 2019.
Nauyin kayan mayen da suka bayyana sun kama ya kai nauyin kilogiram Dari 929 da digo 318 na kayan mayen daban-daban.
Kamar yadda aka sani ne cewa, a halin yanzu matsalar shan kayan mayen na Neman addabar kusan kowa ne sako da lungu a fadin tarayyar Nijeriya saboda ko cikin kauyuka ma duk shaye-shayen kayan mayen duk ya karade.
Sannan wata sabuwa ma za ka ga shaye shayen a halin yanzu ya shiga tsakanin maza da mata, zawarawa da ‘yan mata lamarin da ke bukatar tsananin addu’a tare da bayar da cikkkiyar kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here