Kotu Na Barazanar Daure Shugaban DSS

0
309
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi barzanar daure shugaban hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya Yusuf Bichi, bisa matakin hukumar na kin sakin mawallafin jaridar Sahara Reporters Omoyele Sowore.
A cikin wata takarda da kotun ta fitar ranar Alhamis wadda ta ce ta aika wa hukumar ta DSS, kotun ta bukaci shugaban na DSS da ya bi umurnin kotun ko kuma ya fuskanci fushinta, wanda ka iya hadawa da tsarewa a gidan maza.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai wata kotu a Abuja ta bayar da umurnin sakin Sowore din wanda ake tsare da shi tun cikin watan jiya.
A cewar kotun, tsawon kwanakin da aka dauka ba tare da hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriyar ta saki Omoyele Sowore ba tamkar bijire wa umurnin kotun ne, bayan kuwa wanda aka tsaren ya riga ya cika ka’idojin beli da kotu ta gindaya.
Sai dai hukumar ta DSS ta bakin mai magana da yawunta Peter Afunanya, ta shaida wa manema labarai cewa ba ta samu wata takarda daga kotu da ke umurtar ta da sakin dan rajin mulkin demokradiyyar ba.
A lokacin da na  nemi jin ta bakin mai magana da yawun hukumar ta DSS kan ko sun samu takardar gargadi da kotun ta ce ta aika a jiya Alhamis, ya bayyana mana cewa ba zai so ya ce komai game da wannan al’amari da ke gaban kotu ba.
Bugu da kari mun bukaci sanin ko hukumar na sane da barazanar da kotun take yi na daure shugaban hukumar, nan ma dai mai magana da yawun hukumar ya yi shiru, inda daga karshe ya bukaci da mu ba shi uzurin nema na daga baya game da wadannan batutuwa.
Sai dai har yanzu ba su tuntube mu ba.
Ko a ranar Alhamis dai a wata zantawa da manema labarai  mai magana da yawun hukumar bai fayyace ko za su yi amfani da umurnin kotun ba ko kuma a’a, ko da kuwa sun samu daga baya ba.
Hukumar dai na tsare ne Omoyele Sowore tun bayan da ya shirya wata zanga-zangar da aka yi wa lakabi da revolution now, inda a yanzu hukumomi ke tuhumarsa da laifukan da suka hada da cin amanar kasa, da aibata shugaban kasa da kuma ta’ammauli da kudi ta hanyar da ba ta dace ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here