Makarantar Kangararrun Yara Ba A Kan Zalunci Aka Kafata Ba – Malam El-Kabir

0
385

DAGA WAKILANMU

‘YAN sandan jihar Kaduna sun sami labarin makarantar Attatbiq wadda ake shiryar da kangararrun yara a karkace, ba su yi bincike cikakke ba suka yi wa makarantar dirar mikiya suka cafke malaman makarantar tare da sakin yaran zuwa gidajensu.

Malam Muhammad El-Kabir ne ya fadi haka a yayin hirarsa da wakian GTK a yau Asabar a harabar makarantar inda ya ce ko shakka babu makiyan gaskiya da aikara barna ne suka kai sarar makarantar ga hukuma, ita hukuma ba ta tantance komai ba sai ta auka cikin makarantar don gudanar da aikinta Ya ce makarantar tallafa wa al’umma take ti wajen tarbiyya.Idan kuwa haka ne to, an zalunci makarantar, don kuwa ba a yi masu adalci ba

Ita kuwa rundunar ‘yan sanda ta ce jami’anta sun ceto kusan mutum 500 a wani gini da ake tsare da su a birnin Kaduna.
Baki dayan mutanen dai maza ne, manya da yara, wasu an daure su da mari ko sarka.
Wasu daga ciki ba ‘yan Najeriya ba ne, amma sun ce an gana musu azaba, an ci zarafinsu, an kuma hana su zuwa ko’ina tsawon shekaru, kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo Abubakar ya shaida wa manema.
Babu cikakken bayani a kan yadda suka samu kansu a wurin, ko da yake wasu sun ce kai su aka yi.
Sai dai ana kyautata zaton cewa ginin na makarantar allo ne.
‘Yan sanda sun ce sun kai samame wurin ne, bayan an tsegunta musu cewa ba a gane take-taken mutanen da ke cikin ginin ba.
Kakakin yan sandan ya ce an kama mutum takwas da ake zargin suna da hannu a cikin lamarin.
DSP Yakubu Sabo Abubakar ya ce: “Bayan da muka samu bayanan sirri ne a game da makarantar sai muka kai wannan samame, muka kama shugaban da wasu daga cikin malaman makarantar.
“A yanzu kuma muna gudanar da bincike kafin daukar matakan gurfanar da duk wanda ke da hannu a gaban kotu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here