A’isha Buhari Ta Kwashe Tsawon Watanni 2 Ba Ta Najeriya

0
394

Daga Usman Nasidi.

UWARGIDAN shugaba Buhari wato A’isha Buhari ta kai kimanin watanni biyu yanzu ba ta Najeriya abin da ya fara janyo ce-ce ku-ce a fadar shugaban kasa.

Bayanan da muke samu daga majiya mabanbanta na cewa uwargidan ta bar kasar ne a dalilin yin bore bisa yadda gwamnatin maigidanta ke gudanar da abubuwa a kasar.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa tun dai da uwargidan shugaban kasan ta tafi kasar Saudiyya a farkon watan Agusta domin yin aikin Hajji har yanzu ba ta dawo ba.

Mahajjatan da suka tafi kasar Saudiyya domin sauke farali daga nan Najeriya sun jima da dawowa gida, amma sai dai wata majiya wadda ke da kusanci da Villa ta sanar da mu cewa tun bayan kammala aikin Hajjin uwargidan shugaban kasar ta wuce Landan.

“Mama (wato uwargidan shugaban kasa) tana Landan. Daga Saudiyya ta wuce zuwa birnin Landan,” kamar yadda wata majiyar ta fada mana.

Da kuma aka tambayi majiyar labarin dawowarta sai ta ce: “Ban sani ba, abin da kawai na sani shi ne tana Landan.” An fara lura da cewa lallai ba ta kasar nan kasancewar ana ta yin abubuwan da ya kamata a ganta a wurin amma shiru kake ji.

Bugu da kari, wakilin GTK ya ba mu tabbacin cewa hatta bikin babbar sallah da shugaban kasa ya yi a Daurar jihar Katsina , inda ya yi ta karbar manya-manyan baki, matar tasa ba ta nan.

Gani na karshe da aka yi wa A’isha Buhari shi ne a farkon watan Yuli da suka tarbi jakadiyar Nijar a Najeriya tare da maigidanta shugaba Buhari a Villa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here