Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sauke Shugaban Kotun IST

0
389

Daga Usman Nasidi.

RANAR Alhamis ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sauke shugaban kotun sauraron kararrakin tsaro na hannayen jari (IST), Isiaka Idoko, daga ofishinsa.

Har yanzu dai gwamnatin tarayya bata sanar da dalilin saukesa ba.
Idoko lauya ne daga jihar Kogi ya yi aiki da hukumar SEC ta Najeriya kafin ya yi murabus a 2006 a matsayin darakta.

Har yanzu dai ba mu san ko dalilin zargin rashawa da kungiyar ma’aikatan ke masa ne ya sa aka sauke sa.
IST ma’aikatar shari’a ce mai zaman kanta wacce aka kirkiro karkashin sashi na 224 na dokokin tsaro a 1999.

Rahotanni daga majiya mai karfi daga kotun sauraron kararrakin tsaro da hannayen jarin ta gano cewa Jude Udunni, ne zai maye gurbinsa.

Fusatattun ma’aikatan kotun ne suka mika kara ga EFCC akan zargin rashawa da suke was Idoko.
Kwamitin da aka sa bincike akan zargin basu samo komai ba.

Amma kuma wasikar da babban sakataren tarayya na ma’aikatar kudi, Mahmoud Isa Dutse, ya sa hannu, ta umarci Idoko da ya mika shugabanci ga babban ma’akacin kotun sauraron kararrakin baya da shi.

An zabi shugaban ne a 2017 tare da wasu mutane 9 bayan da kotun sauraron kararrakin tsaro da hannayen jarin ta yi shekaru biyu bata aiki.

Kotun na da kwararren sani a kan kasuwanci, tsaro da dokokin fansho sakamakon kwarewa ma’aikatanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here