Malamai Sun Zama ‘Yan Dako Ga ‘Yan Siyasa – Sakataren JNI

0
326
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKATARE Janar na kungiyar Jama’atun Nasarul Islam Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya ankarar da malamai da limamai da ke jihar Kaduna inda ya yi masu tambaya da cewa yaushe ne malamai suka zama kuma ta yaya za su kasance masu dakon ‘yan siyasa.
Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron tunatar da Malamai da Limamai a kan abubuwan da suka kai jama’a ga halin da ake ciki a yanzu.
Dakta Khalid ya ci gaba da cewa dole sai kowa ya koma ga Allah sannan za a samu gyaruwar lamuran kasa baki daya.
Ya tambayar cewa yaushe ne malamai na addinin Islama suka zama masu dakon ‘yan siyasa? Wanda sakamakon hakan a yanzu ‘yan siyasa sun daina yin kamfe domin a zabe su sai dai kawai su koma wurin malamai domin su yi masu kamfe a tsakanin al’umma.
Ya bayyana halin da ake ciki a yanzu da cewa kowa yana cikin tsoro ne hatta su jami’an tsaron su ma duk tsoron ya kama su, don haka mafita kawai ita ce kowa ya koma ga Allah kasancewa a yanzu babu wani mutum da zai ce ba shi da laifi tsakaninsa da Ubangiji.
Ga yara nan a yanzu sun zama ‘yan sara suka har sai yaro ya rika tabbatarwa da bakinsa cewa ya kashe mutane kaza da bakinsa ba shakka ba kokwanton komai
Ya kara fadakar da malamai da cewa su guji cin abincin haram,matsa wa iyali da karya domin kamar yadda ya ce ba a san malamai da aikata irin wannan ba saboda sai an guje wa irin wannan sannan za a yi addu’a Allah ya karba.
Ya kara da cewa duk ranar da malami ya zama yaron ‘yan siyasa, mai dakon ‘yan siyasa to hakika ya sani lamari fa ya lalace.
“Yanzu haka ‘yan siyasa sun daina yin kamfe sai su dawo wurin malamai su rika yi masu, domin malamai sun zama dilllalai ‘yan dakon kai kaya kawai”.
Ya jefa tambaya da cewa yaushe malamai suka zama ‘yan kore masu dakon ‘yan siyasa?
Ba wani wadansu kwaikwayon da mutum zai yi ya ce shi ba ya laifi, don haka a daina saba alkawari domin Allah ba ya saba alkawari.
Kowa ya tashi tsaye domin gyaran tsakaninsa da Allah a rika bin dokar Allah sau da kada ta yadda za a samu mafita a Nijeriya da duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here