An Banka Wa Mutane 3 Da Ke Zargi Da Garkuwa Da Mutane Wuta

0
338

Daga Usman Nasidi.

A Safiyar jiya Litinin, 30 ga Satumba 2019, wasu matasa suka babbaka wasu mutane uku da ake zargi da laifin garkuwa da mutane a unguwar Dutse Alhaji, birnin tarayyar Abuja.

Mutanen uku da ake zargin sun kunshi maza biyu da mace daya kuma tuni an garzaya da su asibitin Kubwa General Hospital domin jinya.

A wajen, wani jami’in VIO, Aminu Umar, ya bayyana wa manema labarai cewa wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na safe yayin da aka ji ihun wata mata daga cikin mota tana nema dauki.

Ya ce: “Kawai sai aka bankado matar daga cikin matar da suka ga tana ihu. Wani direba wanda ya ga abin da ya faru, sai ya tare motar a gaba, karkashin gadar Dutse.”

“Daga wajen, yan babura suka zagaye motar kuma suka bukace su su fito daga cikin motar.”

“Yayin da suke tambayarsu shin ‘yan kwacen mota ne ko garkuwa da mutane, kafin a ankara sai matasan suka suburbude su da duka kuma suka banka wa motar wuta.”

Wani mai idon shaida mai suna, Aliyu Mohammed, ya ce matasa masu aikin babur di sun bankawa motar wuta ne saboda an gano cewa masu garkuwa da mutane ne bisa ga jawabin matar da suke kwace wa mota

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here