Buhari Ya Yi Kashedi Ga Hukumar Kwastan, FIRS Da DPR A Kan Kudaden Shiga

0
388

Daga Usman Nasidi.

SHUGABA Muhammadu Buhari ya yi kashedi ga hukumonin da ke kawowa gwamnati kudaden shiga inda ya ce idan suka gagara kawo abin da aka shata masu za su fuskanci hukunci matsananci .

Shugaban kasan ya yi wannan maganar ne a yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya game da ranar murnar cika shekaru 59 da samun ‘yancin kan kasar.

Daga cikin hukumomin da wannan hukuncin zai shafa sun hada da hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam, FIRS, DPR da dai sauransu.

“Kokarin da muke ci gaba da yi na samar da tattalin arziki mai inganci kuma yalwatacce shi ne dalilin da ya sa muka hade ma’aikatar kudi da kuma kasafi ta kasa wurin guda.” Inji Buhari.

“Wadannan ma’aikatun guda biyu su ne ke da alhakin kula da duk wani shige da fice da kudade a gwamnatinmu. Ma’aikatun ne ke kula da kudaden shiga da kuma kasuwanci musamman ga masu kananan sana’o’i.

“A don haka ya zama wajibi mu sanya ido ga hukumomin dake tarawa kasar nan kudaden shiga, ta yadda zai kasance komi na tafiya yadda ya kamata. Amma kuma idan muka samu akasin hakan daga wata hukuma to hakika za ta fuskanci hukunci.

“Muradi dai a nan shi ne ya kasance ko wace hukuma ta iya kawo abin da aka yanke mata domin a matsayin kudaden shiga da ya kamata ta kawo.” Inji Shugaban kasa.

Hakazalika, Shugaban kasar ya bayyana cewa ma’aikatar kudi da kasafin kasa na musamman ta fitar da kudi biliyan N600 domin yin wasu manyan ayyukan raya kasa cikin watanni uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here