Dalilin Da Ya Sanya Kotu Ta Kori Karar Abba Gida-Gida

0
344
Rabo Haladu Daga Kaduna
KOTUN da ke sauraron kararrakin zaben watan Maris na 2019, ta ce Gwamna Umar Abdullahi ne zababben Gwamnan jihar Kano a zaben da aka gudanar ranar 23 ga watan Maris.
Mai shari’ar Halima Shamaki ce ta yanke wannan hukunci ranar Laraban nan.
Dan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ne dai ya kalubalanci gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC da yin magudin zabe.
Mai shari’a Shamaki ta ce, ta yi watsi da karar da dan takarar na jam’iyyar PDP ya shigar ne bisa gaza gamsar da kotun cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris.
Halima Shamaki ta kara da cewa jam’iyyar PDP na da ‘yancin daukaka kara a kotun koli, idan har hukuncin bai musu dadi ba, inda ta gargadi magoya da su guji tayar da hankali kasancewar jihar Kano jiharta ce.
Tuni dai magoya bayan gwamna Ganduje suka fara murnar wannan nasara, inda su kuma magoya bayan Abba Kabir Yusuf ke nuna rashin jin dadinsu.
Ganduje ya ci zaben ne na biyu da tazarar kuri’a 35,637 inda jam’iyyarsa ta APC ta samu kuri’a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.
Idan aka hada sakamakon zaben na farko da na biyu, jimilla APC ta samu kuri’a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya ci zaben ne da tazarar kuri’a 8,982.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Kano na ranar Asabar 9 ga watan Maris, a matsayin wanda bai kammala ba, lamarin da ya kai ga zagaye na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here