DSS Sun Kama Abdulrasheed Maina

0
389
Mustapha Imrana Abdullahi
JAMI’AN hukumar tsaron ‘yan sandan farin kaya na DSS ta tabbatar da kama tsohon shugaban hukumar gyaran harkokin Fansho ta kasa domin ko ta kwana Abdulrasheed Maina.
Kamar yadda jami’an tsaron DSS suka bayyana cewa an kama Maina ne a unguwar Utako, kan titin Pennsylvania cikin garin Abuja an kuma gudana da wannan aikin kama shi ne bisa irin rokon da hukumar EFCC ta yi na ganin hukumar tsaron farin kayan su taimaka domin Kama Maina.
An dai Kama Maina ne tare da wani dansa mai shekaru ashirin mai suna Faisal Abdulrasheed Maina,wanda ya yi kokarin ganin aikin kamen bai samu nasara ba amma kuma hanzarinsa ba samu nasara ba ko kadan.
Sai da jami’an tsaron suka kwàce wata karamar bindiga ta fistol kafin a kama shi. Shi dai yana karatu ne a shekarar karshe a jami’ar Kanada da ke Dubai inda yake karantar kimiyyar harkokin sadarwa.
Abubuwan da aka samu tare da wanda aka kama sun hada da karamar bindiga kirar Fistol da harsashi mai rai, mota kirar ranji roba da harsashi ba ya hudawa ( SUV), sai kuma BMW saloon, da kudin kasashen waje da wata na’urar daukar hoto daga sama, da wasu muhimman takardu.
Wanda aka kama da ake zargi tare da duk kayan da aka samu za a mika su ne a hannun hukumar EFCC domin ci gaba da bincike tare da daukar matakin da ya dace.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar da jami’in hulda da jama’a Peter Afunanya,ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a load yaushe suna maraba da irin wannan aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da tsaro a kasa baki daya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here