Hadin Kai Da Kaunar Juna Ne Mafita Ga ‘Yan Nijeriya – Masari

0
371
Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kara fadakar da daukacin al’ummar Nijeriya a kan batun hadin kai da kaunar juna domin kasar tare da mutanen cikinta su samu ci gaban da zai samar da nasara.
Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Alhaji Abdu Labaran Malumfashi, da aka raba wa manema labarai domin bikon murnar cikar Nijeriya shekaru 59, da samun ‘yancin kai.
A cikin takardar Masari ya bayyana wa ‘yan kasar cewa hadin kai da aiki tare ne zai haifar da ci gaban da kowa ke bukata. Ya ci gaba da cewa babu kasar da za ta ci gaba matukar idan Yan kasar na tunani sabanin irin abin da ya dace in ana son kasa ta samu nasara a dukkan fanni.
“In ana son kasar ta ci gaba kamar yadda ake tunani dole ne sai kowa ya yi aiki tukuru wajen bayar da gudunmawarsa ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
“Hakika yana da kyau a samu gyaran akida tare da halayya a aikace domin cimma nasara a kan abin da ya hada mu wuri daya tare da juna a tsawon lokaci da kuma dalilan yin lafiya tare.Inji shi.
Gwamna Masari ya kuma bayyana damuwa a kan irin yadda wani sashe ke nuna halin ko in kula ga duk abin da ya faru ta hanyar cewa ba mu abin ya shafa ba ya ankarar da al’umma cewa irin wannan hali ba abin da zai kai mu ga samun nasara a matsayin al’ummar kasa baki daya.
“A kokarin gina kasa mai karfi kuma wadda za ta hada kawunan jama’a, kada mu sake bambance bambancen ra’ayin da ke tsakanin mu ya haifar mana da matsala.
“Mu tabbatar da yin aiki tukuru ta hanyar hadin kai tsakanin juna ta yadda dukkan abin da ya samu wani bangaren kasa tamkar ya samu kowa ne bangaren kasar ne ta yadda za a fuskanci duk wani kalubale da ka iya tasowa da zai fuskanci kasa, amma idan an kasa yin hakan to zai ba da wani yanayi da zai karade dukkan kasa baki daya.
” Batun masu kai hare hare da sauran kalubalen harkokin tsaro ba su da wata nasara da batun siyasa, addini ko bambancin yare ko kabila, saboda ayyukan ta’addanci ko na bata-gari ba su San wani banbancin kabila,yare ko addini ba.
“Don haka ya dace mu kare kasar mu kafin mu shiga cikin harkokin siyasa saboda dole sai an samu kasa ne za a iya tsayawa takara ko yin shugabanci.
“Ya dace mu kaucewa banbance-banbancen da za su kawo mana matsala ta hanyar yin magana da harshenmu da kuma hadama tare da kalubakantar juna a matsayin mu na ‘yan kasa”.
“Ba daidai ba ne mu kalubalanci dukkan wata kabila baki daya ba ko kuma wani addini ko wani bangaren kasa baki daya domin wani ko wasu mutane sun samu kansu a cikin wata matsalar aikata laifi, hakika ba adalci in an aikata irin wannan.
” Ya dace mu rika kula da irin kananan mu tare da abin da muke aikata wa domin samun kasar da za ta hada mu tare saboda ba za mu rika kokarin magana a kan hadin kan kasa amma muna samun wani abu daban ta fuskar alamu. A dukkan abin da za mu ce ko aikatawa, ya dace ya zama babu wata makarkashiya a boye game da hadin kan kasa’, Gwamnan ya kara karfafawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here