Dan Nijeriya Zai Yi Layin Dogo A Iraki

0
485
Mustapha Imrana Abdullahi
JUDE Igwemezie, Injniya dan Nijeriya ne da ya samu kwangilar aikin gina layin dogo a kasar Iraki na makudan kudi Dala Miliyan dari biyar.
Injiniyan dan Nijeriya ne da ya samu horonsa a kasar Kanada yana rike da aikin da ake ganinsa a matsayin mai muhimmanci ga harkar zirga-zirga da sufuri
Amma kamar yadda bayanin ya fito Injiniya Igwemezie ya ce ba kamar irin yadda yake ta tattaunawa da wasu jami’an Nijeriya ba tsawon lokaci, amma ya tattauna ne tare da samun sa hannun takardar yarjejeniyar.
Igwemezie ya ce samun kwangilar a kasar Iraki wani lamari ne mai saukin gaske, sabanin irin yadda yake ta godo tare da bam baki tsawon lokaci a Nijeriya amma aikin yaki samuwa.
A kasar Iraki na samu kwangilar a kalla dala miliyan dari biyar domin samar masu da layin dogo a kasar.
Igwemezie  shi ne shugaban kamfanin (TransGlobim) na kasa da kasa da aka ba aikin shimfida layin dogon
Kamar yadda jaridar Boss ta wallafa injiniyan dan Nijeriya ya samu horonsa ne a kasar Kanada kuma an san shi a duniyar harkokin Injiniya
Aikin samar da layin dogon na da muhimmanci kwarai ga kasar musamman ganin irin yadda layin dogon zai kai wuri mai fadin gaske a birnin Najaf, abin da aka bayyana da hanyar sufurin da ke da matukar muhimmanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here