Kwastan Na Tara Naira Biliyan 5 A Rana

0
359

Mustapha Imrana Abdullahi

SHUGABAN hukumar kwastan na tarayyar Nijeriya Hameed Ali ya shaida wa ‘yan majalisar tarayya cewa a halin yanzu tun da aka rufe kan iyakokin kasar suna samun nasarar tara kudi Naira Biliyan biyar a rana

Ya tabbatar wa ‘yan majalisar cewa hukumar tasa na samun makudan kudi daga Naira Biliyan 4.7 zuwa Biliyan 5.8 tun da aka rufe kan iyakokin Nijeriya.

Ali  ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin hadin gwiwar ‘yan majalisar dattawa da na wakilai masu kula da harkokin kudi da tsare tsare a majalisar.

Kwamitin na hadin gwiwa ya kuma nemi Gwamnan babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele, da kuma shugaban hukumar da ke kula da shigi da ficin jama’a Muhammadu Baban Dede su bayyana gaban su a ranar Alhamis

Da akwai wata ranar da aka samu nasarar tara kudi sama da Biliyan 9 abin da ba a taba samu a baya ba a duk tarihin hukumar kula da shigowa da kayayyaki cikin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here