Yadda Aka Kashe Mata Aka Jefa ‘Yarta Rijiya A Kano

0
503
Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU mutane da ba a san ko su wane ne ba sun halaka wata mata da ‘yarta mai shekaru uku har lahira, a unguwar Gobirawa ‘yan yashi da ke birnin Kano.
Rudunar ‘yan sandan jihar ta ce an kashe matar ne mai suna Farida Dahiru Abubakar a gidanta, sanna masu kisan suka jefa ‘yarta ‘yar shekara biyu a cikin wata rijiya da ke gidan.
Mai gidan dai ya koma gidan nasa ne da misalin karfe 10 na dare, inda ya buga kofar domin mai dakinsa ta bude masa amma ya ji shiru.
Malam Shu’aibu Abdulmumin ya shaida wa manema labarai cewa “da misalin karfe hudu muka yi waya da ita sai ta ce min ba ta jin dadin jikinta domin ba ma ta iya girka abincin rana ba kuma wannan ce maganata da ita ta karshe.”
“Da na shiga gidan sai na same ta a wani hali na kwance cikin jini wanda sai na ji kamar kaina zai buga amma dai ba zan iya tantance ko yanka ne ko kuma caka mata wuka a kayi ba ta ce tuni suka kama mutum shida da suke zargi na da hannu a faruwar al’amarin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Haruna Kiyawa ya shaida wa manema labarai  cewa bayan kaddamar da wani samame “Mun sami mutum shida da adda da jini a jikinsu kuma tuni mun fara bincike wanda muke son kammalawa cikin kankanin lokaci domin gurfanar da su a gaban kuliya.”
A baya-bayan nan dai ana yawan samun yanayin da ake kashe mutane a cikin gidansu a jihar Kano, inda ko a makon da ya gabata sai da aka samu wasu da suka kona wani mai gida ta matarsa da ‘yarsa.
An dai ce an cinna musu wuta a dakin da suke al’amarin da ya yi sababin mutuwarsu da konewar gidan baki daya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here