Malamai 4,692 Za Su Rubuta Jarabawar TRCN A Kaduna

0
398

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HUKUMAR tantance malaman Najeriya wato TRCN a ranar Juma’a 4 ga watan Oktoba 2019 ta ce malamai 4,692 ne za su rubuta jarabawa a jihar Kaduna domin gwada cancantarsu.

Shugaban TRCN reshen jihar Kaduna Kabir ‘Yar’aduwa ne ya fitar da wannan sanarwa a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce a cibiyoyi uku za a rubuta jarabawar.

Ya kuma kara da cewa jarabawar wadda za a gabatar a kasa gaba daya za ta zo ne a ranar Asabar 12 ga watan Oktoba kuma za a yi amfani da na’ura mai kwakwalwa ne domin rubuta jarabawar.

Malaman da ke zango na uku wato Zone 3 a Kaduna za su rubuta jarabawarsu ne a Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna da ke Gidan Waya, a cewarsa.

Haka kuma a kididdigar da ya ba mu, ya sanar damu cewa malamai 3,820 ne na makarantun firamare yayin da 361 kuwa su ne na makarantun sakandare.

Bugu da kari, akwai mutum 22 wadanda ke karantarwa a makarantun gaba da sakandare yayin da wasu 489 ke rike da shahadar malaman makaranta amma ba koyarwa suke yi ba.

‘Yar’aduwa ya ce: “Idan har muka kammala wannan jarabawa cikin nasara, hakan zai daga yawan malamai masu shaidar TRCN zuwa 63, 128 a jihar Kaduna.”

Shugaban ya bayyana mana cewa hukumar TRCN ta riga ta yi wa malamai 58, 436 rajista a jihar Kaduna. Wannan dalilin ne ya sanya jahar ke sahun gaba a jerin sunayen jihohin dake da malamai masu dauke da rajistar hukumar TRCN, inji ‘Yar’aduwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here