Sace Daliban Kaduna: Sun Fadi Kudin Fansar Da Za A Biya

0
480

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

BARAYIN da suka sace dalibai mata shida na Kwalejin Engravers da ke Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun ce sai an biya su miliyan N50 kafin su saki daliban da malamansu.

A safiyar ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka shiga kwalejin suka yi awon gaba da dalibai mata shida tare da malamai biyu inda suka kai su wurin da ba a san ko ina ba ne har yanzu.

Jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari.

Makarantar wadda ke kauyen Kakau Daji inda daya daga cikin iyayen daliban da aka sacen ke sanar da shi cewa, barayin sun nemi hukumar makarantar ta biya su naira miliyan 50 kan su sako daliban da malamai biyu.

Kamar yadda ya fada mana, daya daga cikin iyayen ya ce: “Mun samu labarin cewa barayin sun tuntubi hukumar kwalejin inda da fari suka bukaci a biya miliyan N30 kudin kowane mutum guda.

“Abin da makarantar ta fada masu shi ne naira 100,000 kawai za ta iya biya domin a sako mata daliban da malamansu guda biyu. Barayin cewa suka yi ba ku shirya karbar dalibanku, idan kun shirya sai ku kira mu.”

Hakazalika, makarantar ta bayar da hutun kar-ta- kwana saboda sace dalibai mata shida da malamai biyu da aka yi a makarantar don gudun faruwar wani mugun abu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here