Shi’a: Ba ma mut’ah da kananan yara

0
853
Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU malamai mabiya mazhabar Shi’a a Nijeriya sun yi karin haske kan auren mut’ah, da wasu mabiya mazhabar suke yi.
Auren na mut’ah dai yana daga abin da musulmai suke da sabani a kansa tun a farko-farkon musulinci.
Ko a ‘yan kwanakin nan manema labarai sun gudanar da wani bincike na musamman kan yadda wasu malaman Shi’a ke gudanar da auren mut’ah da kananan yara a Iraki.
A hirar da manema labarai suka yi da Sheikh Bashir Lawan, wani malami mabiyin mazhabar Shi’a kan wannan rahoto na auren mut’ah, ya ce, auren mutu’ah a wajen ‘yan shi’a aure ne, amma a wurin Ahlussunnah sun ce bai halatta a yi shi ba, domin ya saba wa addini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here