Dan Majalisa Ya Samar Da  Ribar Dimokuradiyya A Mazabunsa

0
345

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

MAKUSANCI ga wakilin Bagwai da  Shanono a majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Isa Legal ya ce ko shakka babu, al’umomin kananan hukumomin Bagwai da Shanono suna samun ribar dimokuradiyya idan aka dubi irin ayyukan alheri da dan majalisa Alhaji Ali Isa  Shanono ya yi a zangon wakilcinsa na farko da kuma wadanda ya fara a zango na biyu domin bunkasa rayuwar mutanen Bagwai da Shanono.

Ya yi wannan bayani ne  a hirar da ya yi da  wakilinmu yayin da ya gabatar da  wasu  muhimman ayyukan raya kasa da dan majalisar ya yi a garin Jaulere, cikin yankin karamar hukumar Shanono, inda ya sanar da cewa dan majalisa Ali Isa Shanono ya yi aikace-aikace masu matukar amfani ga al’umomin mazabar sa, a zangon wakilcin sa na farko, ga shi kuma ya fara  aiwatar da  wasu  ayyukan a zango na biyu domin  kyautata rayuwar al’umar kananan hukumomin Bagwai da Shanono kamar yadda aka fara  gani.

Alhaji Isa Legal ya kara  da  cewa da  yardar Allah dan majalisa Alhaji Ali Isa Shanono zai ci  gaba da  gudanar da  wakilci mai  albarka ta yadda kowane bangare zai sami ribar dimokuradiyya bisa yin la’akari da  bukatun al’umar yankunan kananan hukumomin Bagwai da  Shanono kamar  yadda abin yake  a cikin manufofin sa na aiyukan raya kasa ba tare da nuna banbancin ra’ayi ko na siyasa ba.

Daga karshe, Alhaji Isa Legal ya yi amfani da  wannan dama inda ya gode wa al’umomin Bagwai da  Shanono saboda kaunar da  suke nunawa dan  majalisa Ali Isa Shanono tare da jaddada cewa da yardar Allah, mutanen Bagwai da  Shanono za su rabauta daga ayyukan raya kasa ta kowane fanni cikin shirin ayyukan dan  majalisa kamar yadda aka gani a zangon farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here