IG Ya Yi Kaca-Kaca Da Hukumar PSC Bayan An Aika Wa DIG Sammaci

0
598

Daga Usman Nasidi.

LABARI na zuwa mana cewa wutar yakin da ake yi tsakanin shugaban Dakarun ‘yan sanda Mohammed Adamu da kuma shugabannin hukumar ‘yan sanda na kasa, ta ki mutuwa har yanzu.

IGP Mohammed Adamu ya sake samun kansa cikin rikici ne da hukumar PSC inda ya fada mata cewa ba ta da ikon da za ta aikawa Mataimakansa watau masu mukamin DIG a kasar sammaci.

Sufetan ‘Yan sandan kasar ya fadawa hukumar a wata wasika cewa doka ba ta bata dama ta taba Mataimakan Sufeta Janar ba. IGP yace PSC ba ta da wannan hurumi a dokar da ta kafa ta a 2001.

Shugaban ‘yan sandan yake cewa abin da hukumar za ta iya shi ne karin matsayin ‘yan sanda ko kuma sallamar jami’an da su ka sabawa doka daga bakin aiki wanda shi ma bai shafi taba IGP ba.

Hakan na zuwa ne bayan Hukumar ta PSC ta aikawa DIG Yakubu Jubrin takardar sammaci da cewa ya sabawa dokar aiki. Jubrin shi ne babban mai kula da horas da jami’an sandan kasar.

Sufeta Janar MA Adamu shi ne ya maidawa hukumar martani a madadin DIG Jubrin. PSC ta na ikirarin ta samu DIG din da laifi ne bayan ya fitar da sunayen sababbin Dakarun da aka dauka aiki.

Asalin ta-ta-bur-zar dai a kan batun daukar sababbin ‘yan sanda 10, 000 da za ayi ne a Najeriya. Hukumar PSC ta na ganin cewa ita ke da wannan alhaki yayin da IGP yace aikin sa ne wannan.

A halin yanzu, labarai na yawo cewa IG ya nemi shugaban hukumar PSC, Musiliu Smith, ya dawo da manyan motocin nan kirar Toyota Prado SUV har 8 da aka ba shi kwanaki da nufin ya rika aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here