Masu Garkuwa Da Mutane Sun Saki Mata 13 Daga Katsina

0
380
Mustapha Imrana Abdullahi
MASU Garkuwa da mutane sun saki sauran rukunin mata sha uku kuma rukunin na karshe da aka yi garkuwa da su tare da ‘ya’yansu biyu.
Matan sha uku da wani jinjiri sabon haihuwa da kuma wani dansu mai kimanin shakara daya duk sun kubutar ne daga hannun masu garkuwa da mutane, abin da ya bayyana cewa shi ne samun karshe na wadanda aka yi garkuwa da mutane da su.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Katsina Malam Abdu Labaran ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta muryar Amurka sashin hausa, inda ya tabbatar da cewa wadannan mutane sune samun karshe na mutanen da ake garkuwa da su an kuma sake su ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here