Zamfara Na Samun Koma Baya A Sulhunta Da ‘Yan Bindiga

0
451
Rabo Haladu Daga Kaduna
A daidai lokacin da tattaunawa da ‘yan bindigar jihar Katsina ke samun nasara, har ta kai ga sako ‘yan jihar da akai garkuwa dasu, ita kuma Zamfara ta fara samun koma baya. Hasali ma, ana ci gaba da bayyana alfanu ko rashin alfanun da ke tattare da yin sulhu da ‘yan ta’addan,
Aika aikar ‘yan bindiga a jihohin da ke arewa maso yammacin Najeriya ya kai wasu gwamnoni hawa teburin sulhu da ‘yan ta’addan.
Sulhun na zuwa ne a daidai lokacin da hedikwatar tsaron kasa ke hada hancin baki dayan farmakin da dakarunta ke kai wa ‘yan bindiga da ke kai wa wannan shiyya farmaki, daya kwakkwara mai taken “Operation Hadarin Daji” .
A baya dai gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ziyarci hedikwatar sojojin kasa da na sama inda ya nemi mayakan da su tsagaita wuta, biyo bayan sulhu da ya fara da ‘yan ta’addan.
A cewar Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Baba Abubakar, ba laifi a bi duk wata hanyar da doka ta amince don kawo karshen wannan masifar
Yayin da shirin sulhu da miyagun ke samun tagomashi a jihar Katsina, inda aka sako baki dayan ‘yan jihar da ‘yan ta ‘addan ke garkuwa da su, can a makwabciyarta jihar Zamfara kuwa ‘yan ta’addan ne ke sake kunno kai, duk kuwa da sulhun da aka yi a baya.
Massanin tsaro Dakta Kabiru Adamu da bai goyi bayan irin wannan sulhu ba, ya ce, ‘yan ta’addan yanzu suna ganin tamkar sun fi karfin hukBindiga

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here